ABNA24 : Jaridar “Isra’il Today” da ake bugawa da harshen Hebrewa ta nakalto majiyar gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa tana cewa, nan da wasu makwanni za a yi taron zaman lafiya na larabawa da HKI
Majiyar ta kara da cewa za a yi taron ne a cikin daya daga cikin kasashen larabawan yankin tekun pasha, kuma a halin yanzu Amurka tana kokarin jawo kasashen Bahrain, Oman, Morocco, Sudan da Tchadi da su halarci taron.
Majiyar ta kara da cewa; shugaban gwamnatin kwarya-kwaryar Palasdinu Mahmud Abbas Abu Mazin da jami’an gwamnatinsa sun ki amsa goron gayyatar, sannan kuma su ka aike wa da ministan harkokin wajen Amurka da wasikar cewa kada kafarsa ta kata Ramallah, domin ba a maraba da shi.
342/